BADAKALAR KUDADEN FANSHO: ZAN FASA KWAI IDAN BUHARI YA BA NI KARIYA-MAINA

Tshon shugaban kwamitin farfado da harkokin fansho na kasa, Abdulrashida Maina ya ce a cikin watan Janairun da ya gabata ya taimaka wa gwamnatin shugaba Buhari wajen bankado Naira Tiriliyan daya da miliyan dubu dari uku.

Maina wanda hukumar yaki da zambar kudi ta EFCC ke nema ruwa a jallo, ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da ya aike wa gidan talabijin na Channels.

Har ila yau, ya kara da cewa a lokacin da yake zaune a wata kasar waje, Atoni Janar kuma ministan shara’a, Abubakar Malami ya ziyarce shi inda ya sanar da Malami a kan wannan kudi, Naira Tiriliyan daya da miliyan dubu dari uku

Tsohon shugaban kwamitin na gyara harkokin fansho ya bukaci shugaba Buhari da ya ba shi kariya, domin ya bayyana a zauren majalisar dokoki ta kasa ba tare da an kama shi ba.

Ya ce idan ya samu wannan dama zai bayyana wasu muhimman bayanai da dama da za su amfani gwamnati.

Maina ya kara da cewa wasu daga cikin wadanda ke zagaye da shugaba Buhari ba su fada masa gaskiya a kan abun da ya shafi badakar kudaden fansho.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *