SAMPAOLI YA YI TAIKACIN LALLASA ARGENTINA DA SUPER EAGLES TA YI

Yayin da Najeriya ta lallasa kasar Argentina da ci 4-2 a wasan sada zumunci da aka yi a kasar Rasha a ranar Talata, mai horar da kungiyar kwallon kafa ta kasar Argentina, Jorge Sampaoli ya bayyana damuwarsa a kan kashin da tawagarsa ta sha a hannun Super Eagles.

Ya ce wasa ne mai matukar wahala.“Kamata ya yi a ce mun shiga gaba da ci  uku zuwa hudu tun kafin a tafi hutun rabin lokaci, amma sai muka tafi hutun rabi lokaci muna kan gaba da ci biyu da daya”.

Sampaoli ya ce babbar damuwarsa ita ce yadda ‘yan wasansa suka taka leda a lokacin da Najeriya ke cin Argentina 3-2.

Ya kara da cewa Argentina na da zaratan ‘yan wasa wadanda za su iya fitar da kasar kunya, amma abun takaici hakan bai kasance ba a karawarsu da Najeriya, dan haka wannan abun damuwa ne matuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *