EFCC TA KWATO FIYE DA NAIRA DUBU 700 A CIKIN SHEKARA BIYU

Hukumar yaki da zambar kudi ta kasa EFCC ta bayyana cewa ta yi nasarar kwato kudaden sata kimani Naira miliyan dubu dari bakwai da talatin da takwas da miliyan dari daidai Dalar Amurka miliyan dubu biyu da miliyan dari tara.

Hukumar ta yi nasarar karbar kudaden ne daga watan Mayun shekarar 2015 zuwa Oktoban shekarar 2017.

Mukaddashin shugaban hukumar Ibrahim Magu ne ya bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata wajen babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na bakwai a kan yaki da rashawa da ke gudana yanzu haka a birnin Vienna na kasar Austria.

Kakakin hukumar ta EFCC,  Wilson Uwajaren ne ya bayyana hakan daga cikin jawabin da Ibrahim Magu ya gabatar a wajen taron.

Magu ya ce hukumar ta bankado kudade da dama ta hanyar dabarar karbar kudaden sata ba ta hanyar shara’a ba a karkashin sashe na goma sha bakwai na dokar yaki da rashawa ta shekarar 2006.

Bugu da kari, Magu ya bayyana cewa Najeriya ta samu gagarumin cigaba bangaren batutuwan da suka shafi kudaden tsohon shugaban kasa, marigayi Janar Sani Abacha da badakalar mai ta Malabu da na tsohuwar minister albarkatun man fetur, Diezani Allison Maduekwe da kuma badakar kudaden makaman yaki da kungiyar Boko Haram.

A cikin sanarwa da wilson uwajaren ya fitar, ya ce Najeriya ta samu yabo daga manyan kasashen duniya a kan yadda ta tsaya kai-da-fata wajen bankado kudaden sata da sauran kadarorin da aka mallaka ta hanyar haram.

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *