KUNGIYAR KWADAGO TA BUKACI GWAMNATIN TARAYYA TA KARA ALBASHIN MA’AIKATA

 Shugaban hukumar kwadago ta kasa-NLC reshen jihar Kwara, Abdulyekeen Agunbiade ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake bitar tsarin albashin ma’aikatan gwamnatin kasar nan.

Agunbiade ya yi wannan kira ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Ilorin a kan halin da kasa ke ciki.

Ya ce kungiyar ta NLC na da ra’ayin cewa ya kamata a rika kara albashin ma’aikata duk bayan shekara goma.

Shugaban kungiyar ta NLC reshen jihar Kwara ya cigaba da cewa ma’akatan kasar nan ba za su aminta da karancin albashin da ya gaza Naira dubu hamsin ba.

Ya bayyana cewa kungiyar ta NLC bata yi watsi da fafutukar ganin an kara albashin ma’aikata ba a wannan kasa.

One comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *