YAKI DA RASHAWA: KOTU TA DAGE KARAR DA EFCC KE YI WA IBRAHIM SHEMA

Babbar kortun jihar Katsina ta dage karar da hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta shigar a kan tsohon gwamnan Jihar, Ibrahim Shehu Shema zuwa ranar goma sha uku ga watan Fabarairun shekarar 2018, a game da zargin da ake masa na almubazzaranci da kudaden jihar a lokacin da yake kan mulki.

An gurfanar da Ibrahim Shehu Shema tare da tsohon kwamishinan kananan hukumomi da lamurran masarautun jihar, Alhaji Hamisu Makana da babban sakatare a ma’aikatar, Lawal Safana da kuma tsohon shugaban kungiyar kananan hukumomi na jihar, Lawal Dankaba bisa zargin karkatar da Naira Miliyan dubu goma sha daya a cikin shekara takwas na mulkin Shema.

Idan ba a manta ba dai a baya, Ibrahim Shema ya daukaka karar zuwa kotun daukaka kara da ke Kaduna, inda ya kalubalanci hurumin babbar kotun ta Katsina a kan sauraron karar da ake masa, amma sai kotun ta Kaduna ta ce a sake komawa babbar kotun ta Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *