YAU NE AKE SA RAN ZA A YI JANA’IZAR AVM MUKHTAR MUHAMMAD

Ana sa ran cewa yau ne gawar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Air Vice Marshal Mukhtar Muhammad za ta iso filin tashi da saukar jirage na Malam Aminu Kano da ke Kano.

Wata majiya ta sheda wa Freedom Rediyo cewa marigayi Muhammad wanda ya rasu ne bayan ya yi jinya a wata asibiti da ke Landan kasar Birtaniya, za a dauko shi ne a cikin jirgin rundunar sojin sama ta Najeriya.

Daraktan yada labarai na fadar gwamnatin Kano, Salisu Tanko Yakasai ya ce wata tawagar fadar shugaban kasa ce za ta karbi gawar a hukumance a Kano

Har ila yau, Yakasai ya bayyana cewa za a yi jana’izar mamacin a Kofar Kudu da ke fadar Sarkin Kano

Kafin rasuwarsa, marigayi Mukhtar Muhammad ya kasance ministan ayyuka da raya birane, kana mamba a majalisar koli ta rundunar sojojin Najeriya a shekarar 1975.

Ya kuma yi gwamnan Kaduna daga shekarar 1978 zuwa 1979.

 

 

One comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *